Da Dumi-Dumi Labaran Jiha

Al’adun Hausa na daya daga cikin Nagartattun a Duniya – Hon Arc Abba Yusuf

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Shugaban hukumar kula da guraren tarihi da al’adun na Jihar Kano Hon. Arc Abba Yusuf ya bayyana haka ka lokacin gudanar da horo na musamman ga ma’aikatan hukumar dake kananan hukumomi 44 da ke fadin Jihar Kano.

Yace babu shakka riko da al’adun Hausa na da matukar muhimmanci ga al’ummar Hausawa don haka wajibine ga al’ummar Hausa su Cigaba da koyi da al’adun.

Ya kara da cewar kasashen Duniya da dama suna alfahari da al’adun Hausawa don haka bai kamata a samu hausawa suna watsar da al’adunsu suna runguwar wasu al’adun bakin haure ba.

Hon yayi kira da dukkanin Jami’an da suka samu wannan horo da su tabbata sunyi aiki da ilimin ta hanyar da ya dace don wayar dakan al’ummar jihar Kano akan muhimmancin riko da al’adu.

Kazalika hon ya yabawa Gwamnaatin Jihar Kano bisa bada cikakken hadin kai da goyon baya wajen ganin an farfado da Guraren Tarihi da al’adun jihar Kano, tare da jan hankali akan wasu masu ruwa da tsaki da su guji yin amfani da irin wadanda gurare ta hanyar da bata tace ba.

Shima a nasa Jawabin Sheak Malam Ibrahim Khalid Babban Malamin Addinin Musulunci ya bayyanna Matsayin Addinin Musulunci akan al’adun Hausawa tare da alfanun dake tattare da rikon al’adu.

Leave a Comment