Labaran Jiha

AGILE: Zamu Hada Hannu Da Shirin AGILE Don Bunkasa Harkar Ilimi A Jihar Kano

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

An yi kira ga iyayen yara dake fadin jihar Kano da zu zage dantse wajen kulawa da ilimin ‘ya’yan.

Kiran ya fito ne daga kwamishiniyar ma’aikatar mata,yara da masu. Bikata ta musamman Hajiya Aisha Saji

Saji, ta bayyana hakan yayin da shuwagabannin Shirin nan na Agile suka Kai mata ziyara a lakar aiki a ofishinta.

Saji ta ce, ma’aikatar ta zata hada hannu da Shirin na Agile domin ganin an gudu tare an tsira tare.

Itama a nata jawabin, shugabar Shirin Mai kula da shiya ta biyu na Shirin Agile Hajiya Halima Tukur ta bayyana farin-cikinta bisa fahimtar da ma’aikatar ta yiwa Shirin tare da yabawa Hajiya Aisha Saje bisa fahimtar da goyan baya da ta Basu wajen aiwatar da Shirin a makarantun dake fadin jihar Kano

Tun da fari anasa jawabin mataimakin jagoran Shirin Alhaji Salisu Idris ya bayyana yadda tsarin gudanar da Shirin na agile ya ke ga kwamishiniyar ma’aikatar.

Leave a Comment