Addini

Addu’o’i’n Cigaban Zaman Lafiya

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Gamayyar kungiyoyin Malamai ta Unguwar Gama “E” dake Kaura Goje a karamar hukumar Nassarawa ta gudanar da saukar karatun Alkur’ani maigirma domin gudanar da addu’o’i na musamman ga yankunan da wasu mahimman mutane da suka gabata da jihar Kano baki daya.

Limamin masallacin juma’a na Kaura Goje Mal. Ibrahim ne wanda ya jagoranci taron addu’o’in, inda ya bayyana dalilan da suka sa aka gudanar da saukar karatun Alkur’anin wanda ya gudana a fadar mai unguwar Gama Kaura gojen dake Karamar Hukumar Nassarawa.

Mal. Ibrahim ya bayyana cewa, makasudun gudanar da taron addu’ar a yankin domin yiwa magabata da suka rasu addu’a da yiwa yankunan Unguwar Gama da jihar kano addu’o’i, bisa halin da al’umma suke ciki na matsin rayuwa.

A jawabinsa shugaban shirya taron mai unguwar Gama Kaura Goje Malam Hashimu Rabi’u yace, makasudun taron domin tunawa da mahaifinsa marigayi Mal. Rabiu da yi masa addu’a bisa cikarsa shekaru hudu da hasuwa da yiwa marasa lafiya na gida da asibiti addu’a kamar su maifada mai unguwar Gama B. da tayashi addu’a na cikarsa shekaru goma yana rike da matsayin Mai unguwar Gama Kaura goje.

Malam Hashimu Rabiu, ya bayyana cewa, ba zai manta da maigarin Gama Alh. Rabe bisa irin gudunmawar da yake bayarwa a yankunan Unguwar Gama da Karamar Hukumar Nassarawa ta fannoni da dama a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Haka Zalika, mai unguwar ta Gama Kaura Goje Mal. Hashimu, ya yabawa dukkannin malamai da suke ba shi hadin kai a matsayinsa na shugaban yankin da sauran al’ummar Gama Kaura goje baki daya.

Yace, shugaban ba ya samun nasara a matsayinsa na shugaba ba, har sai in magoya bayansa sun ba shi hadin kai, inda yayi kira ga ‘ya’yan da suka rasa iyayensu, da su kasance masu yi musu addu’o’in samun rahama daga gurin Allah Subahanahu Wata’ala.

Daga karshe yayi fatan Allah ya jikan iyaye da kakanni da sauran al’ummar musulmi da suka gabata da kuma, fatan Allah ya sa mu cika da imani Amin.

Leave a Comment