Kasuwanci

Abu Ne Mai Kyau Tsarin Da Gwamnati Tayi Na Samar Da Dala Ga ‘Yan Kasuwar – Mustafa Naira

Written by Admin

Daga: Kabir Getso

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar canji dake Abuja Alh Muhammad Adam Al’mustafa Naira ya bayyana cewa abu ne mai kyau ga da gwamnati tayi na samar da Dalla ga ‘yan kasuwa wanda hakan yasa yanzu haka farashin Dala din yake sauka

Mustafa Naira ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilin Radio Nigeria Pyramid Kano Kabiru Getso a ofishinsa dake Abuja, yace dama can matakin da gwmanati ya kamata ta dauka kenan na sakin Dala din ga ‘yan kasuwa domin hakan ne zai bada damar saukar farashin Dala din,kamar yadda take sauka a halin yanzu.

Mustafa Naira ya kara da cewar duk da cewar ba kowa ne yake da damar cin gajiyar wannan tsari na samun Dala daga Babban bankin kasa ba ,amma hakan zai taimaka kwarai wajen cigaba da saukar farashin Dala din.

Shugaban ya kuma yi kira da babbar murya ga Ministan Babban Birnin altarayya Abuja Nelson Wike da ya tausawa ‘yan kasuwarsu mara sa karfi da aka tasa a bakin titi, yawancinsu basu da jarin kama shaguna wanda hakan yasa sun zama abin tausayawa da rashin damar cigaba da sana’ar tasu.

Yace suna kira da dukkannin masu rike da madafin iko Sanatoci da ‘yan majalisu da suyi iya kokarinsu wajan samawa wadannan dubbannin Al’umma mafita,daga halin da suka tsinci kansu.

Leave a Comment