Yanzu-Yanzu

Abduljabbar: Kotu ta Sanya Ranar Karbar Rubutattun Hujjojin karshen na Kowanne Bangare

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Mustapha Gambo Muhammad

Babbar kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano, karkashin jagorancin Alkali Ibrahim Sarki Yola ya sanya ranar 29 da watan Satumba, 2022 domin lauyoyi su gabatar mata da rubutattun jawabansu na karshe, a Shari’ar da Gwamnatin Jihar Kano ke tuhumar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

A yayin zaman na ranar Alhamis din nan, kotun ta umarci Jagoran ayarin lauyoyin Mallam Abduljabbar da ya je gidan gyaran hali domin tattauna da shi kuma ya taimake shi domin shirya jawaban kariyar sa na karshe a gaban kotun.

Umarnin hakan dai ya biyo bayan roko ne da malamin yayi a gaban kotun, in da ya shaidawa kotu cewar kwana biyu lauyan ya rabu da ziyartarsa kamar yadda yadda ya saba yi.

Ku karanta: Kotu Ta Ki Amincewa A Mayar Da Shari’ar Abduljabbar Abuja

Lauya da ya halarci zaman don ci gaba da baiwa malamin kariya, Barista Salihu Ibrahim Faki tuna a baya ya roki kotun da ta sallami malamin, inda ya yi zargin cewar babu wata alaka tsakanin sashen dokar da kuma tuhumar da ake yiwa Mallam Abduljabbar.

Ya ce malamin ya yi fassara ne akan hadisan da imamu Malik da Imam Bukhari suka rawaito.

Ya ce ba dai-dai bane a tuhumi malamin da hukuncin batanci tun da a cewarsa ya na maimata abubuwan da aka ruwaito ne.

Sai dai tuni jagoran ayarin lauyoyin Gwamnati, Suraj Sa’ida SAN ya yi suka ga rokan lauyan Abduljabbar inda ya roki kotun da ta amince da duk bayanai da hujjojin da su ka gabatar mata.

A halin da ake ciki dai, Kotun ta baiwa kowanne lauya damar kawo mata rubutattun jawabansu tare da sabunta kowanne bangare a cikin makonni biyu masu zuwa, farawa daga lauyoyin Mallam Abduljabbar.

Leave a Comment