Da Dumi-Dumi

A Shirye Muke Domin Ciyar Da Masarautar Gaya Gaba

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Masarutar Gaya ta sha alwashin nada mutane da suke taimakawa talakawa da marayu da sauran al’umma a mukamai daban-daban da suke masarautar domin yaba musu bisa gudunmawar da suke bayarwa a yankunan.

Maimartaba Sarkin Gaya Alh. Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir ne ya bayyana haka a lokacin da yake nada Alh. Safiyanu Galadima a matsayin Dallatun Gaya da kuma, Alh. Abdulkadir Galadima a matsayin Dangorubar Gaya da Alh. Ibrahim Gwadabe a matsayin Sarkin Tsaftar Gaya, wanda ya gudana a fadarsa dake garin Gaya.

Maimartaba Sarkin yace, nadin irin wadannan mutane zai taimaka gaya wajen ciyar da al’umma gaba ta fannoni da dama.

Yace, makasudun nada wadannan mahimman mutane, a matsayin jagororin kowanne bangare shine, domin a kara musu kwarin gwuiwa da karsashin ci gaba da taimakawa masu karamin karfi na wannan yankuna da kuma, sanyawa wasu sha’awar tallafawa masu bukata a koda yaushe.

Dr. Aliyu ya kara da cewa, Masarutar Gaya ba za ta gajiya ba wajen zakulo irin wadanda suke jibuntar lamarin Alumma da taimakonsu a yayin da bukatar hakan ta taso.

Maimartaban ya yi kira a garesu da su kasance jagorori na gari da za su fara sanya al’amuran al’ummarsu kan gaba wajen ganin sun magancesu.

A jabansu daban daban tun da farko, sun godewa Maimartaba Sarkin Gaya, bisa zabarsu da ya yi a matsayin wadanda za su rike wadannan mukamai na shugabanni masu rike da masarautun gargajiya.

Wadanda aka nada akwai: Alh. Safiyanu Galadima a matsayin Dallatun Gaya, sai Alh. Abdulkadir Galadima a matsayin Dangorubar Gaya da Alh. Ibrahim Gwadabe a matsayin Sarkin Tsaftar Gaya, inda kuma, suka jaddada aniyarsu na ci gaba da taimakawa al’umma da ciyar da Masarautar Gaya da ma yankunan Karamar Hukumar Gaya dake nan jihar Kano.

Leave a Comment