Labaran Jiha

Ina Nan A Raye Ban Mutu Ba

Written by Admin

Daga: Abdulmajid Tukuntawa 

Hajiya Hadiza mahaifiyar jarimar tiktok Murja Ibrahim Kunya wacce a kwanan baya kadan lamarinta ya haifar da cece kuce.

Hajiya hadiza tace, itace mahaifiyar Murja Kuma tana raye ba kamar yadda taji wasu na cewa Murjar iyayenta sun mutu ba. Tace hatta mahaifin ‘yar ta ta wato Malam Ibrahim shima yana raye sai dai lalura da yake fama da ita a gida.

Hadiza tace, baza ta yarda da irin kallon da akewa ‘yar ta ta Murja Ibrahim kunya ba, na cewa wai tana da matsalar kwakwalwa.

Wanda tace daji ana shirin yiwa Murjar allura ta masu rangwaman hankali domin ceto lafiyar ta.

Mahaifiyar Mujar tace, duk abin da aka ga yarta tana yi kawai barkwanci ne Wanda dama tun tana karama ta taso da shi.

Inda ta mika kokon bara ga gwamna Abba Kabir Yusif da sauran masu iko da su shigo cikin wannan lamari don samun daidai to.

Leave a Comment