Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Kano Zata Yi Aiki Kafada Da Kafada Da ‘Yan Jaridu – Dantiye

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Hon. Baba Halilu Dantiye ya bayyana kokarin da kafafen yada labarai keyi don tallata manufofin gwamnati.

Dantiye ya bayyana hakan ne lokacin da Kungiyar Kano youth journalist forum ta kai masa ziyara a Ofishinsa a ranar Juma’a, ace babu shakka aikin jarida aiki ne mai matukar mahimmanci ga cigaban kowace al’umma, don haka wajibi ne gwamnati tayi wani abu da zai taimaki sha’ainin aikin na jarida.

Ya kara da cewar akwai tanade tanade da Gwamnatin tayi shiri akan kyautata aikin Jarida wadanda suka hada da shirya bita ta Musamman, samar da kayan aiki na zamani da sauran Abubuwan da Gwamnatin tayi tanadi, kuma za’a saka kunshin wannan Kungiya a ciki don itama taci gajiya tsarin

Shima a Nasa Jawabin Mai taimakawa Gwamna akan kafafan sada zumunta Hon Salisu Yahaya Hotoro ya bayyana kungiyar a Matsayin wata babbar kungiya da tayi aiki tukuru tun a lokutan zabe don ganin samun nasarar Gwamnatin Engr Abba Kabir Yusif, don haka ya nuna farin cikinsa da yadda Kwamishinan ya karbi kungiyar hannu bibiyu.

Musa Zangida Ma’aikin gidan Radio Premier dake kano wanda shine Shugaban kungiyar ya bayyanna farin cikinsa bisa yadda Suka sami tarba daga Kwamishinan, kuma ya bayyanna cewar a madadin dukkanin ‘ya’yan Kungiyar zasu Cigaba da aiki tukuru domin samun nasarar dorewar Gwamnatin Jihar Kano.

A kalla an samu wakilcin Gidajen Radio 13 wadanda suka halarci ganawar wanda suke cikin kunshin Shugabancin kungiyar da kuna sauran mambobi.

Leave a Comment