Da Dumi-Dumi

Rashin Zuwan Shugabannin Kananan Hukumomi Ofis Kesa Ma’aikata Rashin Zuwa Aiki

Daga: SANI ABDULLAHI DANBALA

Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa reshan Jahar Kano Awamaret Abdullahi Muhammad Gwarzo ne bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa dake helikwatar karamar hukumar birni Kwamaret Gwarzo yace a yanxu kananan hukumomi sun zama kufai saboda rashin zuwa aiki da ba ayi, hakan ne yasa yayi kira ga shugabannin da ma’aikatan dasu mai da hankali wajen cika alkawarin dasu dauka a yayin kama aiki.

Shugaban kungiyar ya kuma lasafto kadan daga cikin irin nasarorin da ya samarwa kungiyar kamar gina babbar shelikwata,da ciyadda ma’aikatan kananan hukumomi zuwa matakin jaha, da karin shekaru ga maaikatan, sai walwala da inganta rayuwar su.

Daga karshe ya yi kira ga gwamnatin Jahar Kano da ta bawa kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin hadin Kai da goyon baya.

Leave a Comment