Yanzu-Yanzu

Masauratar Kano tasha Alwashin taimakawa Matuka motocin Akorikura – Mahmud Bayero.

 

By: Ibrahim Sani Gama

Masarautar Kano ta sha alwashin tallafawa kungiyar matuka motocin Akorikura (NURTW) reshen railway dake nan Kano, cikakkiyar gudunmawar da ta kamata domin ciyar da harkokin sufuri gaba.

Mai girma Hakimin karamar hukumar Fagge Alh Mahmud Ado Bayero Turakin Kano ne ya bayyana haka a lokacin da kungiyar ta kai masa ziyara domin taya shi murna tare da bashi lambar girmamawa, bisa karin girma da ya samu.

Mahmud Ado Bayero, yace, fadar sa a shirye take wajen tallafawa kungiyar matuka motocin Akorikura ta railway, wajen inganta sana’arsu yadda ta kamata, duba da irin jajircewar da ‘yan kungiyar suke da shi a fannin samarwa matasa ayyukan dogaro da kawunansu.

Mai girma Turakin Kano, ya kuma, hori ‘yan kungiyar da su kasance masu bin dokokin tuki da kaucewa gudun ganganci a yayin gudanar da ayyukansu musamman, idan suka hau manyan tituna.

Yace, kofarsu a bude take ga duk wata bukata da kungiyar take nema domin ciyar da harkokin sufuri da kare martabar masarautar Kano da tallafawa matasan jihar Kano ta fannoni da dama.

A jawabinsa shugaban kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen railway dake nan Kano, Abubakar Dan’iya Bala, yace sun kawo zayarar ne domin taya maigirma Hakimi murna bisa Karin girman daya samu daga Tafidan Kano zuwa Turakin Kano, Wanda masarautar Kano ta nadashi karkashin jagorancin mai martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero.

Dan’iya Bala ya kara da cewa, kungiyar tana bukatar fadar Mai girma Hakimin karamar hukumar Fagge, da ta shigewa kungiyar matuka motocin Akorikurar gab, domin Samar mata gurin tsayawa na din din din karkashin Gwamnati.

Shugaban kungiyar yace, duba da gudunmawar da fadar mai girma Hakimin take baiwa kungiyar a Kano, ya karawa kungiyar kaimi wajen bashi lambar girmamawa da taya shi murna bisa karin matsayin daya samu daga masarautar Kano.

Ya jaddada kudirin kungiyar wajen baiwa masarautar Kano hadin kan daya kamata domin kare martabar masarautar Kano da fadar maigirma Hakimin karamar hukumar Fagge.

 

Leave a Comment