Yanzu-Yanzu

Kano ta Kudu: Na karbi kaddarar faduwata zabe – KABIRU GAYA

By: Mukhtar Yahaya Shehu

Sanata Mai wakiltar Kano ta Kudu Kabiru Ibrahim Gaya ya taya Suleiman Abdurraham Kawu Sumaila murnar lashe zabe bayan da ya kayar da shi a zaben da aka gudanar a ranar asabar din da ta gabata.

Cikin wata nadaddiyar muryar da Pyramid Radio ta samu, Sanata Kabiru Gaya na jami’yyar APC ya taya abokin takarar tasa murna ga wanda ya lashe zaben wato Sulaiman Abdrrahman Kawu Sumaila na jami’yyar NNPP inda ya ce bashi da niyar kai kara kotu domin kalubalartar sakamakon zaben.

“Ina godiya ga Allah kasancewar sau 4 ina tsaya wa zaben Sanata Kuma ina samun nasara amma sau daya aka taba kaini kara, saboda haka ba zan Kai kara ba”, inji Sanata Gaya.

 

Leave a Comment